Labarai
Yau za’a tantance Christopher Musa mai ritaya a matsayin sabon Ministan Tsaro a Najeiya

Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana yau Laraba, 3 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar da za’a tantance Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya a matsayin sabon Ministan Tsaro, bayan murabus ɗin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar.
Ta cikin sanarwar da Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce sun karɓi bukatar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu don gaggauta tabbatar da sabon ministan.
Bamidele ya bayyana cewa ba za a jinkirta wannan bukata ba saboda halin da tsaron kasa ke ciki, inda ake bukatar haɗin kan majalisa da fadar shugaban kasa.
Janar Musa, wanda ya sauka daga mukamin sa na shugaban Sojin kasar nan kusan makonni biyar da suka gabata, ya samu wannan amincewar shugaban kasa bisa kwarewa da cancanta a fannin tsaro.
You must be logged in to post a comment Login