Labarai
Yaushe Ganduje zai nada Kwamishinoni?
Yanzu haka watanni biyar kenan da rantsar da wasu gwamnoni da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma kawo yanzu akwai wasu gwamnoni da basu nada kwamishinoni ba cikin kunshin gwamnatin su, ciki har da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
A shekara ta 1999 bayan darewar sa kan karagar mulki a tafarkin dumukuradiyya, tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da aka rantsar da shi a ranar Ashirin da tara ga watan Mayu ya nada kwamishinoni cikin kunshin gwamnatin sa a tsakanin watannin Yuni da Yuli.
Yayin da shi kuma tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya samu nasarar lashe zabe a shekara ta 2003 bai fi wata uku kachal ba ya rantsar da kwamishinoni sa.
Haka zalika, a shekara ta 2007 bayan ya sake dawo zango na biyu Malam Ibrahim Shekaru bai fi wata guda ba ya nada kwamshinoni cikin gwamnatin sa.
Har’ila yau, a shekara ta 2015 gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje bayan da aka rantsar da shi kan mulki a ranar Ashirin da tara ga watan Mayu cikin makwanni biyu ya aike da kunshin sunayen kwamishinonin sa ga majalisar dokoki ta jiha don neman sahalewar su kasancewar hakan mutane suka yi ta mamakin ganin gwamnan a shirye yake.
Amma kuma sai gashi labarin ya sha bambam a wannan lokacin ganin yadda ake ta zuba idanu don ganin suwaye zai nada a matsayin kwamishinonin.
Gwamnonin Kaduna da Sokoto sune a farko-farkon wadanda suka nada kwamishinoni ya zuwa yanzu daga cikin gwamnoni 7 na shiyyar Arewa maso yammacin a kasar nan, yayin da gwamnan Bauchi ne ya fara nada kwamishinoni sa daga cikin jihohi 6 na shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan.
A shiyyar Arewa ta tsakiya kuwa, gwamnonin Kwara da Nasarawa da kuma Filato na daga cikin gwamnonin da ba su fitar da jerin kwamishinonin su ba har yanzu.
Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce har yanzu yana nazarin mutanen da yakamata ya nada a mukaman kwamishinoni, kuma a matsayin ‘yan majalisar zartarwa na jihar nan.
A dai kwanakin baya ne gwamana Ganduje ya ce wa’adinsa na biyu zai sha banban da wa’adin mulkinsa na farko, kuma zai dawo da wasu daga cikin tsoffin kwamishinonin sa wasu kuma ba za su dawo ba, za su fitar da sunayen su nan bada jimawa ba.
Masani kan kimiyar siyasa na jami’ar Bayero ta Kano, kuma mai fashin baki kan al’amuran dumukuradiyya farfesa Kamilu Saminu Fagge yace rashin nada kwamishinoni a gwamnatance nakusu ga cigaban dumukuradiyya baki daya.
Kuma hakan na nuna cewar gwamnan da zai ci karan-sa ba-babbaka ganin haka zai haifar haifar da cin hanci da rsahin
A cewar Farfesa Kamilu Fagge rashin nada kwamishinoni zai ta’allaka akan manyan sakatarori wajen tsunduma su cikin harkokin siyasa babu gaira babu dalili.
Kuma hakan rashin nada kwamishinoni zai sanya ayyukan gwamnati ya dinga tafiyar hawainiya kuma babu wanda zai aiwatar da manyan ayyuka sai gwamna.
Rahotannin sun bayyana cewar, sama da mutane 100 ne da suka hada da ‘yan siyasa, malaman jami’a da sauran kwararru suke ta faman neman a nada su a matsayin Kwamishinoni a Jihar Kano.
Mutanen da suke neman a nada su a matsayin Kwamishinonin sun fito ne daga sassan siyasu mabambanta da suka hada da wasu daga sashen tsohon Gwamnan jihar ta Kano, Malam Ibrahim Shekarau, da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Hafizu Abubakar
Sauran su ne tsohon Kwamishinan muhalli a karkashin gwamnatin Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, da Aminu Dabo.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunan ta dake kusa da gwamnatin jihar, ta shaidawa Freedom Radio cewa, kashi 40 ne kadai na tsofaffin Kwamishinonin jihar ake sa ran dawowarsu a kan mukaman na su.
Kazalika Majiyar ta ce, kashi 60 na tsofafin Kwamishinonin ba za su dawo ba a cikin sabuwar gwamnatin ta Ganduje, sabili da rashin iya tabuka komai a zangon farko na gwamnatin ta Ganduje.
Sai dai wasu na ganin cewar gwamna Ganduje na jan kafa ne domin ya tabbatar da ya yi zabi nagari a cikin jihar, har ma wasu ke zargin yana nazari ne wajen kafa sharuddan irin mutanen da za su kasance a cikin gwamnatin ta sa.
Har ila yau Majiyar ta ce daga cikin sharuddan da ya kafa wajen zaben Kwamishinonin na sa, sun hada da irin kokarin da mutum ya yi a baya, biyayya ta kai tsaye, dagewa, ilimi da kuma kwarewa.
A cewar majiyar duk kuwa wanda bai cika wadannan sharuddan ba, ba zai taba zama kwamishina ba a cikin gwamnatin na shi.
A wannan karon Gwamnan da gaske yake yi a kan nagartar mutanen da zai yi aiki a tare da su a matsayin Kwamishinoni,”in ji Majiyar.
Majiyar ta kara da cewa, gwamnan kuma zai bayar da mahimmanci ne ga mata, a sabbin nade-naden da zai yi na Kwamishinoni, yana mai cewa, mata ne mafiya yawan da za a nada a matsayin Kwamishinoni a jihar.
Ya ce nadin kwanakin baya da aka yi wa mata su 11 a matsayin manyan sakatarori ‘yar manuniya ce da take yin nuni da matan ne za su kasance mafiya yawa a cikin sabbin Kwamishinonin da za a nada.
Majiyar ta kara da cewa, Gwamna Ganduje ya yi alkawarin yin tafiya ne tare da kowa a cikin gwamnatin na shi.