Connect with us

Labarai

An nada kyaftin Rabi’u Yadudu shugaban hukumar FAAN

Published

on

Wata sanarwa  Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya nada Kyaftin Rabiu Hamisu Yadudu a matsayin shugaban hukumar kula da filayen jiragena sama ta kasa,FAAN.

da mukaddashin darakta mai kula da harkokin yada labarai da kuma hulda jama’a a ma’aikatar sufuri ta kasa, Mista James Odaudu ya fitar yau a Abuja ta bayyana nadin sabon shugaban hukumar.

Mista James Odaudu ya ce sabon shugaban hukumar direban jirgin sama ne zai karbi aiki daga hannun tsohon shugaban hukumar, Saleh Dunoma, wanda shi kuma injiniya ne.

Sanarwar ta ce nadin sabon shugaban ya fara aiki ne nan take, wanda kafin sabon mukamin nasa, darakta ne mai kula da ayyuka a hukumar ta kula da filayen jiragen saman na kasa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!