Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yemi Osinbajo:Ya bukaci yan Najeriya da su guji zaben masu sace musu dukiyar kasa

Published

on

Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo yayi kira ga ‘yan Najeriya da su guji sake zaben masu sace dukiyar kasa mai makon hakan su zabi masu gaskiya da sadaukar kai, a yayin babban zabe mai zuwa.

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana hakan a Ado Ekiti, a yayin zauren tattaunawa tare da masu kananan da matsakaitan sana’o’I.

Mataimakin shugaban kasar wanda ya jagoranci masu shirin tallafawa ‘yan kasuwa na Tradermoni a kananan hukumomin Ikere da Omuo da kuma Iworoko, don mika ta’aziyya ga iyalan wandanda suka rasa ran su a yayin hadarin mota da yayi asarar rayuka fuye da 15 a kwanan baya.

Yemi Osinbajo ya kara da cewar gwamnatin Muhammadu Buhari ta dokufa wajen karfafawa matasa karfin gwiwa na yin kananan sana’o’I, don dogaro da kan su.

Ya ce gwamnati mai ci ta sami nasarar aiwatar da ayyukan raya kasa da suka hada da aikin gina layin dogo daga Lagos zuwa Kano da Calabar zuwa Asaba ya dangana zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!