Kasuwanci
Yin amfani da abincin gargajiya zai bunkasa al’ada: Sarkin Kano
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce ‘amfani da abincin gargajiya ga al’umma zai kara fito da muhimmancin Al’ada da kuma cimakar bahaushe.
Sarkin Kano ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai wajen da ake gudanar da bikin bajakolin abincin gargajiya da ke guda a harabar fadar Masarautar ta Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna farin cikinsa bisa dabbaka darajar abincin gargajiyar domin dada nuna mahimmancin al’adar Hausa.
Wakilin mu na Masarautar Kano Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa, Sarkin Yana tare da rakiyar sakataran sa Alhaji Isah Sanusi Bayero.
Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login