Labarai
Za a ci gaba da aiwatar da sabbin dokokin haraji daga 1 ga Janairun 2026- Minista

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiwatar da sabbin dokokin haraji daga ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara mai kamawa kamar yadda aka tsara.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce an bi dukkan ka’idoji, ciki har da shawarwari masu fadi, tattaunawar majalisa, amincewa da kuma sanya hannun Shugaban Kasa.
Ministan, ya jaddada cewa dokar haraji guda daya ce kacal da aka amince da ita, wadda Majalisar Tarayya ta zartar kuma Shugaban Kasa ya sanya wa hannu.
You must be logged in to post a comment Login