Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a sasanta rikicin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i

Published

on

Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin sunayen kwamitocin karta-kwana da za su sasanta rikicin da ke tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i.

Kwamitocin za su ziyarci wasu makarantun gaba da sakandire na kasar nan don sasanta sabani da ake yawan samu tsakanin magabatan makarantun.

ministan ilimi Malam Adamu Adamu ne tabbatar da hakan, yana mai cewa an kafa kwamitoci guda ashirin da biyar kuma za su ziyarci kwalejojin fasaha na tarayya da kuma wasu kwamitocin guda ashirin da daya wadanda zasu kai ziyara kwalejojin ilimi na tarayya.

Ya ce, shugaba Buhari ne ya amince da kafa kwamitocin don magance matsalolin da ake yawan samu tsakanin masu ruwa da tsaki game da gudanarwar makarantun na gaba da sakandire.

Kuma na bai wa kwamitocin wa’adin makwanni shida da suka kammala aikinsu kuma su mikawa gwamnati sakamakon rahotonsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!