Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a yi jana’izar Sarkin Zazzau da ƙarfe 5 na yamma

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce, za a yi jana’izar marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris CFR da ƙarfe 5 na yammacin yau Lahadi.

Gwamnan jihar Malam Nasir El-rufai ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce a yayin jana’izar za a ɗauki dukkan matakan kariya daga cutar Coronavirus.

 

El-rufa’i ya ce, tuni ya sanar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan wannan babban rashi, haka kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari shi ne zai jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa ta’aziyya garin Zariya.

Gwamnan ya nuna kaɗuwar sa da rashin sarkin, tare da yi masa addu’ar dacewa da aljannar Fiddausi.

Marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris mai shekaru 84 ya rasu a yau Lahadi da rana, bayan gajeruwar rashin lafiya a asibitin sojoji na 44 dake Kaduna.

A watan Fabrairun wannan shekara ne marigayin ya cika shekaru 45 a kan mulki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!