Labarai
Za mu ɗau mataki ga duk wanda muka kama da almundahanar ciyarwa azumi-Gwamnan Kano
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jin daɗin sa bisa yadda ake ciyar da al’umma abinci da gwamnati ta bayar na ciyarwar Ramadan.
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana rashin jin dadinsa kan tsarin ciyarwa da gwamnati ta bayar a wannan watan na Ramadan da ake yi a cikin jihar Kano.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a.
Gwamnan ya ce ya ji babu daɗi a lokacin da ya kai ziyarar bazata ɗaya daga cikin guraren da ake bayar da abinci da ke unguwar Gidan Maza, a ƙaramar hukumar Birni.
Gwamna Yusuf ya kuma nuna rashin jin daɗin sa da yadda masu gudanar da tsarin ke gudanar da shi ba yadda gwamnati ta tsara ba.
“Ba za mu amince da rashin gaskiya da almubazzaranci da dukiyar al’umma ba, ya zama wajibi a lura da cewa kudaden da aka ware don wannan tsarin an tabbatar anyiwa al’umma abin da ya kamata, a cewar Gwamnan.
Gwamnan ya gudanar da ziyarar ne biyo bayan rahoton sirri da ke nuna nakasu wajen gudanar da tsarin ciyarwar a cibiyoyi daban-daban dake faɗin jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login