Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu aiwatar da duk hukuncin da kotu ta zartar a kan wanda ya kashe Hanifa – Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da cewa da zarar kotu ta yankewa mutumin nan da ake zargi da kisan Hanifa za a zartar masa ba da dadewa ba.

Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyayen Hanifa da yammacin ranar Litinin a zanatawarsa da Wakilyar Freedom Radio Zahrau Nasir.

Gwamna ya kuma ce, za a tabbatar an gudanar da shari’a ta gaskiya domin kuwa duk abinda kotu ta yanke gwamnati za ta aiwatar da shi.

“Wannan al’amari sai dai mu ce Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un domin kuwa ba mu taɓa ganin irin wannan tashin hankali ba, kuma lamari ne da ya shafi dukkanin al’ummar ƙasa ba iya jihar Kano ba” a cewar Ganduje.

Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kuma ce, a yanzu haka an kafa kwamitin da zai bada shawara a kan matakan da za a ɗauka a makarantu masu zaman kan su don kare afkuwar hakan a gaba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!