Labarai
Za mu cigaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a kano – Gwamna Abba
Shugaban hafsan sojin sama Air Vice Marshal Hasan Bala Abubakar ya yaba da irin goyon bayan da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke ba shi na ƙarfafa aikinta a jihar.
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin tofa ya fitar, ta ce Air Marshal Abubakar ya yi wannan yabon ne a ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin dake Kano.
Babban hafsan hafsan sojin sama ya bayyana hadin gwiwar sojojin sa tare da saauran jami’an tsaro wajen yakar barazanar tsaro a Kano, inda ya ce sun samu gagarumar nasara tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Air Mashal Abubakar ya lura da tasirin da jami’an sojin saman Najeriya suka yi a wasu ayyuka da suka kai wajen kama ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane haɗin gwiwa da jami’an DSS wa’inda ake nema ruwa a jallo a Kano.
Ya kuma tabbatar wa gwamnatin jihar cewa NAF a shirye ta ke ta ɗaurar da kwanciyar hankali a cikin gida da wajen kano
Ya kuma buƙaci goyon bayan Gwamna wajen hada hannu da gwamnati domin samar da ruwan sha a cibiyar NAF da ke jihar kano domin samun ruwan sha.
Da yake mayar da martani, gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin haɗin gwiwa da rundunar sojojin saman Najeriya domin gudanar da ayyukanta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Gwamna Yusuf ya bayyana muhimmiyar rawar da sojojin saman Najeriya ke takawa wajen samar da tsaro a bangaren sama da kuma baiwa sojojin kasa kariya daga makiyan ciki da waje.
Gwamnan ya jaddada irin gudunmawar da rundunar sojin sama da sauran sojoji ke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a Kano, ya kuma tabbatar da aniyar gwamnatin sa na ci gaba da kulla alaƙa a tsakanin hukumomi.
Haka kuma Gwamnan ya bukaci a kafa makarantar sakandare ta ‘yan mata ta rundunar Sojan Sama a Kano da kuma dawo da makarantar sakandaren maza dake Kwa, cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa. A cewarsa,
“Gwamnatin Kano tana alfahari da ku, kuma muna alfahari da wannan mukami da aka naɗa a bisa kwarewa da sanin makamar aiki, Kano kuma tana alfahari da ƙoƙarin ku na magance matsalolin tsaro musamman matsalar masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da sauran masu laifi.
“Tun lokacin da muka karbi ragamar shugabancin gwamnati, gwamnati na samun kyakkyawar alaka da goyon baya daga rundunar sojojin sama da jami’an tsaro ƴan sanda wanda hakan ne ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.
You must be logged in to post a comment Login