Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Abba ya buƙaci sarakunan Kano da su haɗa kai da hukumomin tsaro

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga sarakunan gargajiya da su hada kai da gwamnati da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Wannan na ƙunshe ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar 23 ga watan Maris 2024

A yayin buda baki tare da sarakuna da ƴan majalisar su daga masarautun jihar 5, gwamnan ya jaddada muhimmancin da sarakunan gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankunansu, inda ya bayyana muhimmancin shigar da su cikin wannan muhimmin aiki.

Gwamna Yusuf ya koka da yadda al’adun gargajiya na da ke ƙokarin kididdiga na al’amuransu, wanda a baya ya taimaka wajen sa ido sosai kan zirga-zirga a yankunan su gida da waje.

Ya kuma jaddada muhimmancin sake farfado da wannan ɗabi’a domin ƙara sa ido kan al’umma da matakan tsaro, inda ya kuma bayyana tsare-tsaren gwamnatinsa na gudanar da atisayen kirga gidaje domin tantance yawan jama’ar gida daidai gwargwado domin tsara ababen more rayuwa da kuma kula da harkokin tsaro.

Bugu da kari, Gwamna Yusuf ya bukaci sarakunan gargajiya da su kara zage damtse da addu’o’i ga jihar da kasa baki daya, yana mai jaddada musu goyon bayan gwamnatinsa na ba su damar sauke nauyin da ya rataya a wuyan su.

A nasu martanin, sarakunan da suka haɗar da na Rano, Alhaji Kabir Muhammad Inuwa, da na Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim, da Karaye, Alhaji Ibrahim Abubakar, sun nuna jin dadinsu da karramawar da gwamnan ya yi musu a lokacin buda baki da suka yi na azumin watan Ramadan tare da yin alkawarin ba su cikakken goyon baya kan manufofi da tsare-tsare da suka sa a gaba wajen inganta tsaro da samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!