Labarai
Za mu daina karatun NCE Jami’ar Sa’adatu Rimi
Shugabancin jami’ar Sa’adatu Rimi dake jihar Kano ta ce nan da shekara biyar masu zuwa za su ga yihuwar ganin ci gaba da karatun NCE a makarantar domin yanzu makarantar ta dashi daga matsayin kwaleji ta koma jami’a mai zaman kanta.
Shugaban Makarantar Farfesa Yahaya Isah Bunkure ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da Freedom Radio.
Bunkure ya ce duk wasu masu karatun NCE da suke cikin makarantar an basu wa’adin shekara biyar domin su kammala kana daga bisani aga akwai yihuwar ci gaba da karatun NCE ko kuwa makarantar zata haƙura illa bayar da shedar Digiri.
Kuma yanzu haka wannan jami’ar ta cika dukkan nin ƙaƙidojin da ake buƙata wajen zama jami’a, domin tana da jajirtaccun malamai da cibiyoyin karatu daban-daban ,A cewar Bunkure.
An samar da wannan jami’ar ne akan har koyarwa, adan haka koda mutun yayi digiri a cikin wannan makaranta yana da damar da zaije ya koyar a firamare ko sakandare, domin dama jami’ar koyar da ilimi ce, wannan bazai bayar da matsala ba wajen ci gaba da yaye malaman makaranta ba.
Farfesan yace zuwa wancan lokacin da aka ware indai har jami’ar bazata iya ci gaba da karatun NCE ba to an sahale mata da ta ware wani sashi na ci gaba koyon dabarun koyarwa, ko kuma akafa wata kwalejin ilimi ƙarƙashin jami’ar ta Sa’adatu Rimi.
You must be logged in to post a comment Login