Labarai
Muna sane da matsalar da al’umma suke ciki a kano na rashin ruwa zata zama tarihi- Gwamna Abba
Gwamnatin jihar Kano ta ce matsalar ruwa sha da ake fama da ita a jihar Kano nan da ɗan ƙaramin lokaci zata zama tari a faɗin jihar, domin kuwa tana sane da matsalar da al’umma suke fuskanta na rashin ruwan.
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne yayi wannan jawabin da yammacin yau juma’a yayin ziyarar gani da ido da ya kai matatar ruwa dake tamburawa domin magance matsalar rashin ruwan a wannan lokaci.
Gwamna Yusuf ya kuma sha alwashin tabbatar da an magance wannan matsala da ake fuskanta inda al’umma ke ta kokawa, dan haka muke fatan al’ummar jihar zasuyi duba da irin matsalar da wannan matatar ruwa ta samu kuma yanzu haka gwamnatin zata tabbatar da an magance matsalar.
Haka kuma ya ƙara da cewa gwamnati zata samar da sababbin injina domin ƙara kaucewa daga wannan matsala da ake fuskanta a wannan lokaci.
Haka kuma gwamnan yace ya zama wajibi gwamnati ta samarwa da al’ummar da take jagoranta duk wasu abubuwa da suke a hakku akan ta.
You must be logged in to post a comment Login