Kasuwanci
Za mu fara bibiyar ayyukan Kamfanoni tare da cafke masu gurɓata kaya- FCCPC

Hukumar kula da gasa da kare haƙƙin masu sayen kayayyaki ta Tarayya FCCPC, ta sha alwashin sanya ido kan kamfanoni da ayyukansu har ma da mutanen da ke yin Al-gus tare da sayar wa mutane gurɓatattun kaya.
Kwamishina mai kula da harkokin yau da kullum a hukumar Hajiya Ummusalma Isiyaka Rabi’u, ce ta bayyana hakan yau Juma’a yayin ziyarar da ta kawo nan Kano domin inganta ofishin hukumar.
Hajiya Ummusalma Isiyaka Rabi’u, ta ƙara da cewa, za su ƙaddamar da kwamitin da zai jagoranci aikin, domin magance matsalolin da Kwastomomi ke fuskanta idan suka saya kaya marasa kyau.
Hajiya Ummusalma Isiyaka Rabi’u, ta ƙara da cewa ” Babban aikin wannan hukumar shi ne, kare hakki da kuma samar da gamsuwa ga masu siyan kayayyaki a duk faɗin Najeriya, don haka ba za mu bari a riƙa cutar mutane ba.”
“Muna da shirin nan ba da jimawa ba kwamitinmu zai fara aikin don fara kamawa tare da gurfanar da masu siyar da gurɓatattun kaya.”
“Yanzu haka wannan ofishi namu na Kano ya inganta sosai, kun ga yadda ake ta yi masa gyare-gyare tare da samar da kayan aiki da na’urori na zamani.”
“A hukumar kula da gasa da kare haƙƙin masu sayen kayayyaki ta Tarayya FCCPC, muna da hanyoyi da dama da mutane za su iya gabatar mana da korafinsu, ko dai su kira mu a waya, ko ta kafafen mu na sada zumunta, ko ma ta hanyar shafinmu na Internet, KO kuma su garzayo ofishinmu duk lokacin da suke da ƙorafi.”
You must be logged in to post a comment Login