Kasuwanci
Za mu gina kasuwannin sayar da Gwal da ta sayar da Magungunan Gargajiya- Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta gina wasu sabbin kasuwanni guda biyu da suka hada da kasuwar sayar da Gwalagwalai zalla da kasuwar sayar da Magungunan gargajiya.
Kwamishinan harkokin kasuwanci da zuba Jari na Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana hakan yau a taron rantsar da sabbin shuwagabannin Cibiyar Kasuwanci ta Kano KACCIMA da aka gudanar.
Haka kuma kwamishinan, ya ce, gwamnatin Kano za ta hada kai da cibiyar ta KACCIMA domin ganin harkokin kasuwanci sun bunƙasa a faɗin jihar Kano.
Ambasada Usman Hamza Darma shi ne sabon shugaban Cibiyar ta KACCIMA, ya ce, za su duba kowanne bangare na harkokin kasuwanci a fadin jihar Kano domin ganin sun kawo gyare-gyaren da za su bunkasa harkokin kasuwanci.
A nasa bangaren Alhaji Ado Muhammad wanda ya jagoranci kwamitin gudanar da zabe na Maslaha a Cibiyar ta KACCIMA ya yi wa sabbin shugabannin fatan nasara a bisa jagorancin da suka karba tare da yi musu addu’ar samun nasara.
You must be logged in to post a comment Login