Labarai
Za mu gudanar da bincike bisa Hatsarin yan wasan Kano- FRSC

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC ta ce zata gudanar da bincike na musamman dan gano musabbabin faruwar hadarin motar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 22 yan Kano da suka wakilci jihar a gasar wasanni ta Kasa da aka gudanar a jihar Ogun.
Shugaban hukumar na Kasa Shehu Muhammad, ne ya bayyana hakan lokacin da tawagar hukumar suka kai ziyarar ta’aziya da jaje a gidan gwamnatin Kano.
Shugaban hukumar ta FRSC, wanda mukadashinsa mai lura da shiyya ta daya da ke jihar Kaduna Ahmad Umar, ya wakilta, ya kara da cewar, hukumar ta fara gudanar da bincike kan musabbabin yaawan faruwar hatsari a gadar ta Yan kifi da ke Kan titin Kaduna zuwa Kano.
Ahmad Umar, ya Kuma ce za su hada kai da gwamnatin Kano da sauran jihohi wajen daukar matakan da suka kamata bayan fitowar sakamakon binciken da suka gudanar don maganace matsalar da ake samu sakamakon yawan haduran.
A nasa jawabin mukaddashin Gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya wakilta ya gode wa hukumar tare da yin alkawarin gudanar da aiki tare da hukumar don kauce wa faruwar makamancin hatsarin a gaba.
You must be logged in to post a comment Login