Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu gyara titunan da suka lalace a sanadin damuna – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace zata gyara titunan jihar Kano da suka lalace musamman ma sanadiyyar damuna.

Manajan darakatan hukumar kula da  gyaren titunan Idris Wada Sale Dawakin tofa Kano ne ya bayyana hakan a yau ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya Kara da cewa a yanzu haka daga titunan da suka lalace sun yi nasarar gyara guda 18 ya yin da kuma suke kokarin cigaba da gyara wasu 13 nan ba da jimawa ba

Ya Kara da cewa duba da yadda gwamnati  ta damu kan  lalacewar wasu titunan ne yasa gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya umarce su da Fara gyare-gyaren tun daga lokacin damuna.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa daga titunan 13 da za’a fara gyaran su nan ba da jimawa ba, sun hada da titin da ya taso daga kofar Naisa zuwa kwanar Diso da Titin Tafawa Balewa da titin Sharada , da titin Ibrahim taiwo da sauran su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!