Labarai
Za mu hada kai da Turkiyya domin yakar rashin tsaro – Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta nemi taimakon kasar Turkiyya wajen yakar matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan Nijeriya.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin tattaunawa da wata tawagar kungiyar Kiristoci ta Nijeriya a gidansa da ke jihar Legas.
Sanarwar da hadiminsa Bayo Onanuga ya fitar, ta ce ya bukaci samun hadin kai daga kungiyar, musamman wajen hakuri da kuma fahimtar irin matakan da gwamnatinsa ke dauka.
Kazalika ya jaddada kudurin kafa ‘yansandan jihohi, a daidai lokacin da gwamnati ke kan aikin hadin gwiwa da kasar Amurka wajen yakar matsalar tsaro, kamar yadda gidan Talabijin na Channels TV ya ruwaito.
You must be logged in to post a comment Login