Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Za mu saki kuɗaɗen ƙungiyar ASUU – Buhari

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce, nan ba da jimawa ba babban bankin kasa CBN zai saki kuɗaɗen ƙungiyar malaman jami’o’i a ƙasar nan.

ƙaramin ministan ilimi Emeka Nwajiuba ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da jaridar Punch.

Ya ce, a yanzu ƙoƙarin da gwamnati ke yi bai wuce na ganin ta saki kuɗaɗen ƙungiyar ASUU da suke bin ta ba.

Ya kuma musanta zargin ƙungiyar na cewa gwamnati ta ƙi cika alƙawuran da suka kulla.

Wanan ya biyo bayan barazanar da ƙungiyar ASUU ta yi na sake tsunduma yajin aiki matukar gwamnatin ta gaza cika alƙawuran su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!