ilimi
Za mu sama wa malamai fiye da 2,000 filaye- ASUSS

Kungiyar Malaman makarantun sakandare ASUSS shiyyar Kano, ta ce za ta samar da filaye fiye da guda Dubu Biyu ga mambobinta a kokarinta na saukaka wa malamai wajen mallakar muhalli.
Shugaban kungiyar Kwamared Abdu Usman Yalo, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da freedom Radio a wani bangare bikin ranar Malamai ta duniya.
Kwamared Abdu Yalo ya kuma bukaci gwamnatin jihar Kano da ta sanya wa Malamai alawus karshen kowanne wata domin kara inganta ayyukansu.
You must be logged in to post a comment Login