ilimi
Za mu sauya tunanin matasan Kano daga shaye-shaye da ayyukan daba- Dr. Abubakar
Kwalejin fasaha ta Kano, ta sha alwashin tallafa wa harkar yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, da ayyukan daba a fadin jihar.
Shugaban kwalejin Dakta Abubakar Umar Faruk, ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da manema labarai a ofishin sa.
Ya ce, kwalejin ta Kano Poly ta duƙufa wajen koyar da matasa maza da mata sana’o’in da za su dogaro da kan su bayan kammala karatu.
Dakta Abubakar ya ƙara da cewa matuƙar al’umma za su rungumi ilimin fasaha a matsayin hanyar samun aikin yi, to kuwa za a rage yawan aikata laifuka a jihar Kano da ma kasa baƙi ɗaya.
Daga nan sai ya buƙaci ƴan kasuwa da masu sana’ar hannu a faɗin jihar Kano da sauran jihohin ƙasar nan da su fito da tsare-tsare da don cin gajiyar duk wani tallafi da gwamnati da ƙungiyoyin agaji ke bayarwa.
Kamar yadda sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na kwalejin Auwal Isma’il Ɓagwai ya fitar ta bayyana.
You must be logged in to post a comment Login