Labarai
Za mu yi aiki da ƙungiyar AOWD wajen tallafa wa mabuƙata a Arewa- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayya, ta sha alwashin tallafa wa al’ummar shiyyar Arewa maso yaammacin kasar nan musamman marasa karfi da masu bukata ta musamman har ma da almajirai domin dakile talauci da kuma magance kalubalen da ake fuskanta a tsakanin jinsi.
Babban mai taimaka wa shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin mutane masu bukata ta musamman tare da bayar da cikakkiyar dama ga kowa, Kwamared Muhammad Abba Isah, ne ya bayyana hakan yayin day a karbi bakuncin kungiyar rajin tallafa wa marayu da tallafa wa mata watau Alkhairi Orphanage and Women Development yayin da ta kai masa ziyara a Abuja.
Kwamared Muhammad Abba Isah, ya kuma tabbatar da yin aiki kafada da kafada da kungiyar domin yaki da cin zarafin jinsi da kuma tallafa wa al’umma musamman domin su dogara da kansu.
Haka kuma ya bayyana irin gudunmawar da ofishinsa ke bayarwa wajen tallafa wa mutane masu bukata ta musamman da kuma rukunin mutanen da ke karkashin kulawar sa inda ya ce, ofishin nasa na lura ne da mutane masu buƙata ta musamman da Almajirai har ma da al’umma marasa ƙarfi.
” Zuwa wannan ƙungiya abu ne da ya zo lokacin da ya dace, mun lura da cewa ta na da ƙididdigar mutane masu buƙata ta musamman da marasa karfi, don haka za mu yi aiki da su wajen rabon tallafi ga waɗanda suka cancanta.”
A nata bangare, babbar Daraktar kungiyar ta Alkhairi Orphanage and Women Development Kwamared Ruƙayya Abdurrahman, cewa ta yi sun kai ziyara ne domin kulla alakar aiki da ofishin na mai Magana da yawun shugaba Tinubu kan lamuran mutane masu bukata ta musamman domin yin aiki tare wajen tabbatar da cewa mabukatan na amfana da tallafi yadda ya kamata.
Haka kuma babbar Daraktar ƙungiyar ta gudanar a alkhairi Orphanage and Women Development, Kwamared Rukayya Abdurrahman, ta kuma jaddada kudurin kungiyar na ci gaba da tallafa wa mata da matasa musmman ta fannin horas das u sana’o’in dogaro da kai tare da basu tallafi.
You must be logged in to post a comment Login