Connect with us

Labarai

Za mu yi aiki tare da sauran gidajen masarautun Zazzau – Sarkin Zazzau

Published

on

Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya sha alwashin yin aiki tare da sauran gidajen masarautar ta Zazzau a dukkannin harkokin mulkinsa.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ke yabawa sabon sarkin biyo bayan kokarinsa wajen hada kan ‘yan uwansa bayan zamansa sarki na 19 a masarautar ta Zazzau.

Yanzu-yanzu: El-rufa’i ya naɗa sabon sarkin Zazzau

Za a yi jana’izar Sarkin Zazzau da ƙarfe 5 na yamma

Nasir El-Rufa’i ya kuma nusar da sarkin game da muhimmancin amfanin hadin kai wajen samun nasarar jagorantar al’ummar Zazzau.

Gwamnan ya bukaci sarkin da ya mai da hankali wajen aiki tare da ‘yan majalisar masarautar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!