Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu yiwa PDP garanbawul da zarar mun koma cikinta – Ghali Na’abba

Published

on

Tsohon shugaban majalisar wakilai ta ƙasa Ghali Umar Na’abba, ya ce mutuƙar suka dawo jami’iyyar PDP babu shakka za su yi mata garanbawul.

Ghali Na’abba ya bayyana haka ne a zantawarsa da Freedom Radio.

“Mun fahimci a cikin jam’iyyar a yanzu ana bautar da wasu ƴaƴan cikin ta, ta hanyar rashin ba su damar su ta gudanar da harkokin jami’iyyar”.

“Abin da zai ba ku mamaki kusan siyasar yanzu ta zama kamfani yadda ta yadda za kaga an baiwa wane kaso kaza, iya biyayyar ka iya jin daɗin ka da ita” a cewar Na’abba

Har ma yayi zargin cewa “Haka kawai sai mutum ya tara mutane yana nunawa a mataayin ƴan jam’iyya ana bashi kuɗi duk da sunan za su kawo gyara”.

Ghali Na’abba ya ƙara da cewa “saboda lalacewa anzo lokacin da ake rabon kason muƙamin jam’iyya, wanda za kaga kowa ya na kawo mutanensa kuma a saka su cikin jerin shugabanci”.

Ghali Umar Na’abba dai ya taɓa wakiltar ƙaramar hukumar birni a zauren majalisar tarayya daga shekarar 1999 a karkashin jami’iyyar PDP.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!