Connect with us

Kiwon Lafiya

Za’a gudanar da tsaftar muhalli na karshen watan nan – Kabiru Getso

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da ranakun juma’a da asabar na karshen wata wajen tsaftace muhallan su musamman a wannan lokaci na damuna a wani mataki na magance matsalar ambaliyar ruwa.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan a yau, ta cikin sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ma’aikatar Abbas Habib Abbas jim kadan bayan kammala ganawa da masu ruwa da tsaki don yin shirye shiryen zagayen tsaftar muhalli da za a gudanar a karshen watannan.

Yace, zagayen tsaftar muhalli an dakatar da shi tsawon lokaci sakamakon annobar Corona wadda da shafi al’amuran rayuwar yau da kullum.

Dr Kabiru Ibrahim Getso ya Kara da cewa sai dai a waccan lokaci gwamanati tayo amfani da damar ta wajen gudanar da feshin maganin kariya daga cutar corona a makarantu da tashoshi da kasuwanni da nasallatai da sauran guraren ibada.

Yana Mai cewa a yanzu ma’aikatar muhalli ta shirya gudanar da zagayen tsaftar muhalli a gobe jumaa a wasu daga cikin kasuwannin jihar sai Kuma ranar asabar da za a gudanar da tsaftar titina da sauran unguwanni.

Dr Getso ya bukaci jamaar jihar Kano su bada hadin Kai daga karfe bakwai na safe zuwa goma na safiyar ranakun jumaa da asabar don tsaftace muhallin su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,784 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!