Connect with us

Kiwon Lafiya

Za’a tilastawa ma’aikatan gwamnati amfani da jirgin Nigerian air da zarar an kaddamar da ita

Published

on

A kokarinta na ganin an bunkasa harkokin Sufurin Jirgin saman kasar nan gwamnatin tarayya ta sanar da fara wani yunkuri na tilastawa ma’aikatanta tafiye-tafiye ta sabon kamfanin da aka kaddamar na kasa Nigeria Air.

Karamin Ministan Sufurin Jiragen sama Hadi Sirika ya ce gwamnatin tarayya ganin Majalisun tarayya sun yi dokar da za ta tilasta hakan don ganin komai ya tafi yadda aka tsara.

Ministan ya bayyana cewa ba didai ba ne yadda wasu ke cece-ku-ce da takaddama dangane da inganci da kuma ‘yancin sunan kamfanin, kamar yadda wasu ke muhawara a kai a shafukan zumunta na zamani.

Ya kuma kara da cewa batun yarjejeniyar da gwamnatin ta kulla da ‘yan kasuwa abu ne mai kyau da zai haifar da ‘da mai ido cikin kankanin lokaci matukar harkokin suka kankama.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,761 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!