Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar sojin Najeriya zata kafa sansanonin gudanar da aiki guda 5 karkashin runduna ta 82

Published

on

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Yusuf Tukur Buratai, ya amince da kafa sansanonin gudanar da aiki guda biyar karkashin runduna ta 82 dake jihar Enugu.

Rahotanni sun ce sababbun sansanonin da za a gina zasu kasance ne a kan iyakokin kasar nan tun daga jihar Taraba zuwa yankin Bakassi wanda ya ke karkashin rundunar ta 82.

Babban kwamandan rundunaar Manjo Janar Adamu Abubakar, ya fadawa manema labarai a jihar ta Enugu yau Lahadi cewar sabbin sansanonin zasu taimaka mutuka wajen bunkasa harkokin tsaro musamman yankunan dake fuskantar barazanar batagari.

Manjo Janar Adamu Abubakar, ya jinjinawa Laftanal Janar Buratai bisa wannan hanke nesa kasancewar wurin kan iyaka ne kuma dake fuskantar barazanar tsaro.

Ya ce bisa kokarin jami’an rundunar tasa a wannan yanki, an samu mutukar raguwar aikata laifuka yan shekarun nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,734 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!