Connect with us

Manyan Labarai

Zaben 2023: Ba zan sake tsayawa takara ba- Shugaba Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari yace tsarin mulkin Najeriya bai ba shi damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan a karo na uku ba.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari  ya bayyana hakan ne a taron kwamitin zartarwa wadda jam’iyyarsa ta APC ta gudanar a birnin Abuja.

Maganar da shugaban kasar yayi ta sabawa rade radin da ake ta yi cewa shugaban kasar wanda wa’adin mulkin sa zai kare a shekarar 2023 na shirin canja tsarin mulkin Najeriya domin tsayawa takarar shugaban kasa a karo na uku.

Amma da yake yiwa jami’an jam’iyyar tasa jawabi shugaba Muhammadu Buhari yayi kira gare su da su zage dantse wajen nasarar jamiyyar ta APC ,inda yace abun kunya ne jam’iyyar ta APC ta ruguje bayan kamala wa’adin mulkin sa a shekarar 2023 .

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,958 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!