Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zaka Iya Zama Da Mai Tarin TB Idan Kai Rigakafi: Rahama

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta samar da shiri na musamman da zai rinka wayar da kan mutane irin illar da cutar Tarin TB yake da shi, musamman wajen saurin yaduwar sa a tsakanin al’umma.

Daraktan sashin bibiyar yaduwar cutuka a ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano, Hamza Shu’aibu Fagge ne ya bayyana hakan a lokacin da Gidauniyar Rahama Girls Child and human Empowerment Initiative ta shirya shiri na musamman domin wayar da kan mutane illar da cutar ta ke da shi.

Ya Kuma ce cutar TB tana yaduwane a cikin Iska idan mutum na amfani da magunguna cutar zai saka a dakile yaduwar ta.

Da yake jawabi shugaban shirin wayar da kan mutane illar da cutar Tarin na TV yake da shi a Gidauniyar ta Rahama Shamsuddin Lawan Muhammad ya ce koda mutum baya dauke da cutar ya zama wajibi ya Nemi maganin da zai Kare Kansa daga kamuwar ta.

Daya daga cikin masu wayar da kan mutane illar da cutar ta ke da Ita Hajiya Maryam Abdurrahman Tijjani cewa ta yi idan mutum ya Sha maganin kariyar kamuwa daga cutar zai iya shekaru 13 Yana mu’amula da Mai ita ba tare da ya dauka ba.

Yayin Taron ma’aikatan Lafiya daga sassa daban daban ne sukayi jawabi kan Irin illar da cutar Tarin fukar ta ke da Ita.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!