Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zalinci da kama karya ke haddasa juyin mulki a Afrika – Farfesa Kamilu Fagge

Published

on

Masanin kimiyyar siyasa da mu’amalar ƙasa da ƙasa a jami’ar Bayero da ke Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce, zalinci da kama karya da wasu shugabanni a nahiyar Afrika ke yi ne ya ke haifar da juyin mulki.

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.

Ya ce, akwai dalilai da ya ake samun juyin mulki musamman a wasu ƙasashen da ke nahiyar Afrika kuma barazana ce ga ci gaban dimokoradiyya har ma da zaman lafiya.

“Za mu iya cewa akwai batun cin hanci da rashawa da ake zargin wasu shugabanni na aikatawa musamman a Afrika wanda kuma na gaba wajen haifar da juyin mulki” a cewa Fagge.

“Sai kuma kama karya da gwamnatoci ke yi da nufin samun damar ci gaba da jagorantar ƙasashensu ko da kuwa sun shafe shekaru da dama suna mulkin ƙasar”

“Na uku kuma zamu ce tashe-tashen hankula wanda ya ke faruwa samakon maguɗin zaɓe da ake gudanarwa da hakan zai kawo naƙasu ga ci gaban kowacce dimokoradiyya”‘ a cewar Farfesa Kamilu Sani Fagge.

Ya kara da cewa juyin mulkin da ya faru a kasar Sudan na nuni da cewa akwai barazanar samun ci gaba da juyin mulkin a ƙasashen Afrika idan akai duba da ga shekarar  1960-1980 an ta samun juyin mulkin a nahiyar.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa matuƙar ana so a samu sauƙin juyin mulkin da ke faruwa to sai gwamnatoci sun runguma ɗabi’ar son ƙasa da kishin ta da kuma tabbatar da  shugabanci na gari ga al’ummar da suke jagoranta.

Wannnan dai na zuwa ne bayan da sojiji a kasar Sudan suka ayyana shugaban gwamnatin haɗaka karkashin Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan bayan juyin mulki da suka gudanar a ranar Litinin.

Kafin juyin mulki a ƙasar Sudan an gano yadda sojoji suka yi juyin mulki a ƙasashin Mali da Guinea.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!