Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu biya ƴan kwangila domin kammala 5 kilometers na ƙananan hukumomi 44

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata biya dukkanin ƴan kwangilar da suke bin gwamnatin kuɗi ha’a biya su ba musamman musuyin aikin 5 kilometers na ƙananan hukumomi 44 na faɗin jihar.

Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da ƴan kwangilar da suke gudanar da aikin 5 kilometers a faɗar gwamnatin Kano.

Gwamna Yusuf ya kuma bayar da umarnin duk wani ɗan kwangila da rashin kuɗi ya hana shi ci gaba da aiki to ya hanzarta kawo takardar sa domin bashi kuɗin da zai ci gaba da aiki.

Kasancewar a wasu daga cikin ƴan kwangilar sun fara aiki a ƙalla kaso 30 wasu kuma ya kai kaso 60 amma rashin biyan su kuɗaɗe ya sanya su dakatawa a cewar Gwamna Abba.

Ka zalika gwamnatin tace zata mayar da hankali wajen ganin an kammala ayyukan 5 kilomita na ƙananan hukumomi 44 dake faɗin jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!