Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu fara binciken yan majalisu zagaye na uku-ICPC

Published

on

Hukumar yaki da ci hanci da rashawa ta ICPC ta kasa, ta sanar da fara binciken aiyyukan ‘yan majalisun tarayya karo na uku a yau.

Mai magana da yawun hukumar Uwargida Azuka Ogugua,ce ta bayyana hakan a Abuja.

Ta ce an fara gudanar da bibiyar aiyyukan ne karo na farko tun shekarar 2019, a jihohi 12 na kasar nan.

Azuka tace a karo na farko an duba aiyyuka 524, ya yinda a karo na biyu aka duba 822 a jihohi 16, da aka kwato Biliyoyin nairori da akayi almundahar aikin su.

Aikin bibiyar da binciken karo na uku yanzu za a gudanar da shi jihohi 17, da suka hada da Katsina , Kano, Sokoto, Yobe da Adamawa da Plateau da Kogi.

Sauran jihohin, sun hadar da Benue sai Ondo da Osun da Lagos, da Bayelsa da Akwa Ibom da Enugu sai Edo da Imo da Birnin tarayya Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!