Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu samar da karin na’urorin lura da tsaro a filayen jiragen saman Najeriya-FAAN

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce za ta kara samar da karin na’urorin dake inganta tsaro a filayen jiragen saman kasar nan.

Shugaban hukumar lura da zirga-zirgar jiragen sama na kasa FAAN Kyaftin Rabiu Yadudu, ne ya bayyana hakan jiya a birnin tarayya Abuja.

Ya ce ya zama dole hukumar ta kara sanya idanu a filayen jiragen saman kasar nan, domin magance batagarin da ke kokarin aikata ta’addanci a filayen jiragen saman.

Yadudu, ya ce irin wannan mataki da gwamnati ta dauka zai taimaka mata wajen inganta dabarunta na dakile matsalar rashin tsaro a harkar sufurin jiragen sama.

Haka zalika ya ce hukumar za ta ci gaba da aiki-kafada da kafada da jami’an tsaron domin ganin harkokin zirga-zirgar jiragen sama ta ci gaba da tafiya yadda ya kamata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!