Labarai
Zan kammala biyan tsoffin Kansiloli hakkinsu nan da karshen wata mai zuwa- Gwamna Abba

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce, nan da karshen wata mai kamawa gwamnatinsa za ta kammala biyan dukkan hakkokin tsoffin Kansilolin Kano da suka yi aiki a tsakanin shekara ta 2014 zuwa 2023.
Gwamna Abba ya bayyana hakan ne a Alhamsi din makon nan, yayin taron da aka gudanar na bayar da kudaden tsoffin Kansiloli har fiye da naira biliyan biyar ga Kansilolin da suka yi aiki daga shekarar 2018 zuwa 2020.
Gwamna Abba ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da rikon amana da gaskiya a dukkanin al’amura, domin ciyar da jihar gaba cikin hadin kai da zaman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login