Labarai
Zan koma Majalisa ranar Talata- Sanata Natasha

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana cewa za ta koma majalisar dattijai a gobe Talata, bayan hukuncin kotu da ya soke dakatarwar da aka yi mata.
A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, Sanatar ta gode wa magoya bayanta bisa jajircewarsu, tana mai cewa wannan hukunci babbar nasara ce ga dimokuraɗiyya.
A cewar babbar kotun tarayya da ke Abuja, dakatarwar da majalisar ta yi mata ta sabawa kundin tsarin mulki, kuma ta tauye ‘yancin wakilcin jama’arta. Kotun ta umarci a dawo da ita bakin aikinta nan take.
Sai dai kotun ta ci tarar Sanatar Akpoti-Uduaghan Naira milyan Biyar, saboda kin bin umarnin da aka bayar a baya. Wannan ya biyo bayan wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Facebook, duk da cewa kotun ta haramta mata yin hakan a baya.
You must be logged in to post a comment Login