Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zargin ɓata suna: Kotu ta ce a tsalala bulala ga Mubarak Unique Picking da maja bakinsa

Published

on

Kotun Majistare mai Lamba 58 ta yanke hukuncin tsalala bulala goma ga Mubarak Muhammad da aka fi sa ni da Unique Picking da mai ja masa baƙi Nazifi Isa Muhammad.

A zaman kotun na yau Litinin, ƙarƙashin jagorancin mai sharia Aminu Gabari ta ce, Mubarak da mai ja masa baki Nazifi za su biya tarar Naira dubu 10 ga kowanne laifi.

Haka kuma kotun ta ce, daga yanzu za su riƙa share kotun na tsawon wata ɗaya.

Daga ƙarshe ma kotun ta umarcesu da wallafa wani bidiyon da za su wanke gwamna Ganduje bisa ɓatancin da suka yi masa.

Tunda fari dai an gurfanar da Mubarak Muhammad da aka fi sa ni da Unique Picking da mai ja masa baki Nazifi Isa Muhammad a gaban kotu bisa tuhumar haɗa kai da ɓata suna ga gwamna Ganduje.

Cikin wani bidiyo da suka wallafa a shafinsu na Tiktok, kuma bayan karanto musu laifin sun amsa da bakinsu, kamar yadda wakilinmu na Aminu Abdu Bakanoma ya rawaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!