Labarai
Zargin kisan kai: Abdulmalik Tanko ya musanta kashe ɗalibarsa Hanifa
Babbar kotun jihar Kano mai lamba 5 ta ci gaba da sauraron shari’ar zargin kisan kai da ake yiwa malamin makarantar nan Abdulmalik Tanko da Hashim da kuma Fatima wajen yin hadin kai tare da sace ta kuma daga karshe suka kashe ta.
An dai gurfanar da su karkashin mai sharia Usman Na-abba a yau Litinin ƙarƙashin mai sharia Barista Musa Abdullahi Lawal wanda ya jagoranci lauyoyi 9, yayin da Lauyan masu kariya Barista M.L.Usman ya jagoranci lauyoyi 5.
Tun da fari dai an karanto musu tuhuma guda biyar waɗanda suka hada da zargin haɗa kai da ɓoye yarinyar, kuma anan take suka amsa laifin yin haɗin kan wajen sace ta amma ita Fatima ta musanta duk tuhumar da aka yi musu.
A nan ne mai gabatar da ƙara ya roƙi kotun a kan cewa a basu dama za su kawo shaidu, shi ma kuma Lauyan da yake kare su ya roƙi a basu bayanan shari’ar, daga nan ne kuma kotun ta amince aka ɗaga shari’ar.
Lauyan waɗanda ake ƙara yayi bayani kamar haka jim kadan bayan fitowa daga kotun.
Wakilin Freedom Radio Aminu Abdu Bakanoma ya rawaito cewa Lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a Barista Musa Abdullahi Lawal ya roƙi a basu wata ranar inda aka ɗage zuwa 2 da 3 ga watan Maris na shekarar 2022 domin kawo shaidunsu.
You must be logged in to post a comment Login