Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zargin murɗiya: Gwamnatin Neja ta dakatar da zaɓen sabon Sarkin Kontagora.

Published

on

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya yi watsi da naɗin sabon Sarkin Kontagora.

Wannan dai ya biyo bayan ƙarar da wasu ƴan takara 46 suka shigar kan zargin murɗiya da rufa-rufa da aka yi a zaɓen.

Haka zalika gwamnan ya sauke kwamishanan harkokin sarakunan gargajiya Abdulmalim Sarkin-Daji, wanda ake zargi da murdiyan.

Tun a ranar Lahadi, an sanar da babban dan kasuwa Mohammadu Barau-Mu’azu matsayin sabon sarkin Kontagora, bayan samun rinjaye a zaɓen da masu zaɓen sarki 5 suka kaɗa.

Amma daga sanarwar sauran ƴan takara suka fara zanga-zanga inda suka zargi kwamishana sarkin-Daji da rufa-rufa.

 

 

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!