Labarai
Zargin safarar ƙwaya: Zainab Kila da ta taɓa zaman kaso a Saudiyya ta zama jami’ar NDLEA
Matashiyar nan Zainab Aliyu Kila da ta taɓa zaman gidan kaso a ƙAsar Saudiyya sakamakon zarginta da safarar ƙwayoyi ta zama jami’ar hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA.
Zainab Aliyu Kila ta samu aiki a hukumar NDLEA ne bayan kammala karatun ta a jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano.
Ɗalibar ta samu nasarar shiga jerin sababbin ma’aikatan da hukumar NDLEA ta ɗauka, inda ta samu matsayin babbar jami’a wato Narcotic Officer.
Tun da fari gwamnatin ƙasar Saudiyya ta kama Zainab Kila a watan Disamban shekarar 2018 lokacin da ta je yin ibadar Umrah tare da mahaifiyarta da ƴan uwanta.
Anan ne jami’an tsaron ƙasar Saudiyya suka zargeta da safarar ƙwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka gano ƙwayoyin a wata jaka mai ɗauke da sunanta.
Sai dai daga baya da aka zurfafa bincike hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta NDLEA ta gano cewa wasu ma’aikata ne a filin jirgin saman Malam Aminu Kano suka saka mata ƙwayar a jakarta.
Tuni dai shafukan sadarwa na zamani musamman shafin Facebook, ya cika da hotunan matashiyar wadda yar asalin jihar Jigawa ce da ke zaune a Kano.
You must be logged in to post a comment Login