Connect with us

Labarai

Ziyarar Tinubu zuwa Birtaniya za ta farfaɗo da alaƙar ƙasashen biyu – Farfesa

Published

on

Wani Farfesa a fannin Tsaro da Dabarun Yaƙi a Cibiyar Koyon Aikin Soja ta Najeriya da ke Kaduna, Nigerian Defence Academy, Farfesa Abiodun Oluwadare, ya bayyana cewa ziyarar aiki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai Birtaniya za ta zama wata muhimmiyar kafa a sabunta alaƙar Najeriya da Birtaniya. Ya ce gayyatar na zuwa ne kusan bayan shekaru arba’in da aka yi irin wannan mu’amala ta matakin koli tsakanin ƙasashen biyu.

 

Farfesan ya ce ziyarar za ta buɗe ƙofofi wajen tattauna bunƙasa kasuwanci da jawo hannun jarin waje, musamman a fannoni kamar fasaha, makamashi mai sabuntawa, noma, ilimi da gine-ginen fasahar zamani. Ya ƙara da cewa haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin fasaha na Birtaniya da jami’o’in Najeriya zai taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi ga matasa tare da samar da hanyoyin ƙaura ta halal da tsare-tsaren saka hannun jari daga ‘yan ƙasar da ke zaune a ƙetare.

 

Haka kuma, ya jaddada muhimmancin ƙarfafa haɗin gwiwa kan yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi, cin hanci da rashawa da kuma manyan laifukan ƙasa-da-ƙasa. A cewarsa, ya kamata a inganta musayar bayanan sirri, horaswa kan yaƙi da ta’addanci da tsaron intanet, tare da tsara kyakkyawan tsarin tafiyar da harkokin ƙaura domin amfanin ɓangarorin biyu, wanda zai taimaka wajen samar da zaman lafiya, ci gaba da wadata a ƙasashen biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!