Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zulum ya kai ziyarar jajantawa ga iyalan jami’an tsaron da suka rasu

Published

on

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kai ziyarar jajantawa ga iyalan jami’an tsaron da suka rasa rayukan su da ma wadanda suka jikkata sakamakon harin da aka kai wa tawagarsa a ranar Juma’ar da ta gabata a yankin Baga.

Hakan na cikin wata sanarwar ce da mai bai wa gwamnan shawara kan yada labarai Malam Isah Gusau ya fitar a jiya Litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa tun a jiya Litinin gwamna Zulum ya kai ziyarar jajantawa ga iyalan jami’an tsaron tare da yi musu alkawarin zai ci gaba da basu kulawar da ta dace don inganta rayuwarsu.

Ta cikin sanarwar ta bayyana cewa, gwamnan ya bayyana takaicinsa kan harin da yayi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaron sa, inda ya yi fatan samun rahma ga wadanda suka rasa rayukan su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!