Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƙarin mutum guda ya kamu da Corona a Kano

Published

on

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce an sami karin mutum guda da ya kamu da Coronavirus a jiya Litinin bayan da aka yiwa mutane 77 gwajin cutar.

Ma’aikatar ta tabbatar da hakan ne ta shafin ta na Twitter, kamar yadda ta saba tana mai cewa a jimlacce dai cutar ta kama mutane dubu 1,743 cikin su kuma dubu 1, 682 sun warke sai guda 54 da suka rasa ransu.

A kasa baki daya kuwa hukumar dakile yaduwar cututtukar ta kasa NCDC ta ce an sami karin mutane 119 cikin jihohi 6 da suka hadar da Lagos da Birnin Tarayya Abuja, Jihar Edo da jihar Oyo nan Kano sai kuma jihar Nasarawa Oyo.

A yanzu haka dai cutar ta kama mutane dubu 62,111 cikin su kuma guda 57,571 sai guda 1,132 da suka rasu a dalilin cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!