Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Ƙasar nan za ta iya fuskantar yanayi irin na Afghanistan – El-rufa’i

Published

on

Gwamnan jihar kaduna Malam Nasir El-rufa’i ya ce, ƙasar nan za ta iya fuskantar yanayi irin wanda Afghanistan ta fuskanta a baya-bayan nan.

Gwamna El-rufai ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da majalisar tattalin arzikin ƙasa a Abuja, wanda mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta

El-rufa’i y ace, zuba jari mai yawa a ɓangaren ilimi shi ne hanya ɗaya da za a magance matsalolin zamantakewa da tattalin arzikin ƙasar nan.

Gwamnan ya kuma ce, matuƙar yan siyasa ba su mayar da hankali wajen ba da gudunmawa a ɓangaren ilimi musammana a Arewacin ƙasar nan ba, to kuwa za a iya tsintar kai a yanayi irin wanda Afghanistan ta tsinci kan ta a ciki.

Har ma ya bayyana mamakin sa kan yadda gwamnonin jihohin ƙasar nan ba sa sanya hannun jarin su a cikin sha’anin ilimi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!