Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƙidayar jama’a: Za a kashe sama da biliyan 190 a 2022

Published

on

Majalisar dattijai ta ce, an ware sama da Naira biliyan 190 domin gudanar da ƙidayar jama’a a shekarar 2022.

Kwamitin majalisar mai kula da yawan jama’a da tantance ƴan kasa ne ya bayyana hakan ta bakin shugaban kwamatin, Sanata Sahabi Alhaji Ya’u jim kaɗan bayan kare kasafin kudin 2022.

Sanata Ya’u ya ce sama da Naira biliyan 190 aka warewa aikin ƙidayar jama’a, kuma da zarar shugaban kasa ya amince za a fara gudanar da ayyukan.

Ko da aka tambaye kan cewa lokacin ƙidayar ya yi daidai da lokacin zaɓe? shugaban kwamitin Ya’u ya ce, sai da aka yi tunani mai kyau sannan aka gano lokacin ne mafi dacewar ayi ƙidaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!