Labarai
Ƙudurin gyaran dokar ofishin mai binciken kuɗi na Kano ya tsallake karatu na biyu
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2020/01/Majalisa-BASHI.jpg)
Ƙudurin gyaran dokar ofishin mai binciken kuɗi na baɗi na jihar Kano, ya tsallake karatu na biyu a zauren Majalisar dokoki ta jiha.
Ƙudurin dai ya kai wannan mataki ne a zaman majalisar na yau Talata bayan da shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari wakilin ƙaramar hukumar Warawa ya gabatar da karatun na biyu.
A Litinin ɗin makon jiya ne dai akawun majalisar Alhaji Garba Baƙo Gezawa, ya gabatar da karatu na ɗaya na dokar.
Za mu kawo muku cikakken labarin a nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login