Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan bindiga ba su yada zango a yanki na ba – Masarautar Ƙaraye

Published

on

Masarautar Ƙaraye ta yi Allah wadai da wani labari da ake yaɗawa a kafar sada zumunta cewar wai ƴan ta’adda daga jihohin Katsina da Zamfara sun shiga yankin.

Har ma labarin ke cewa ƴan bindigar sun yi sansani a wuraren da ake haƙar ma’adinai ba bisa ma’ida ba a wasu Gundumomi uku da ke Masarautar.

Hakan na cikin sanarwar da jami’in yaɗa labaran masarautar Haruna Gunduwawa ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce, labarin da ake yaɗawa bashi da tushe ballantana makama, domin kuwa wasu mutane ne kawai suka kitsa shi da nufin cusa tsoro da zullumi a zukatan al’umma don cimma burin su.

Masarautar ta yi kira ga al’ummar masarautar da na jihar Kano baki ɗaya da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da hakokinsu kamar yadda suka saba domin kuwa tuni gwamnati ta ɗauki matakan kyautata tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!