Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Najeriya za ta kawo ƙarshen matsalar sauyin yanayi nan da 2060 – Buhari

Published

on

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya ce, Najeriya za ta iya kawo karshen matsalolin gurabatar yanayi nan da shekarar 2060.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan a shafin na Facebook.

Ya ce, shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a babban taron sauyin yanayi da ake gudanarwa a birnin Glasgow na kasar Scotland.

Sai dai ya ce, yaki da sauyin yanayi yana bukatar isasshen tallafi ta bangaren fasaha da kudi musamman a kasashe masu tasowa.

Tun da farko dai, shugaba Buhari ya shaidawa wakilan da suka halarci taron sauyin yanayi cewa, dole ne sakamakon taron ya gaggauta amfani da duk wasu batutuwan da suka shafi yarjejeniyar da aka kulla da kasar Faransa.

Shugaban Muhammadu Buhari dai ya bi sahun wasu shugabannin kasashen duniya da suka hada da shugaban kasar Amurka Joe Biden, Fira minisatan Burtaniya Boris Johnson, da na Indiya Narendra Modi, da na Kanada Justin Trudeau da dai sauransu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!