Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan bindiga sun aurar da ƴaƴan mu – Iyayen ɗaliban makarantar sakandiren tarayya da ke Yawuri a jihar Kebbi

Published

on

Iyayen ɗalibai ƴan makarantar sakandiren gwamnatin tarayya da ke garin Yawuri a jihar Kebbi sun bayyana cewa ƴan bindiga da suka sace musu ƴaƴa a kwanakin baya sun sanar dasu cewa tuni sun fara aurar da ƴaƴan nasu a tsakaninsu

 

Wasu daga cikin iyayen yaran sun ce ƴan bindigar sun turo musu da faifan bidiyo wanda a ciki suna nuno yadda aka aurar da ƴaƴansu.

 

Makwanni biyu da suka gabata ne wasu ƴan bindiga suka sace ɗaliban na makarantar gwamnatin tarayya da ke Yawuri a jihar Kebbi.

 

A zantawa da gidan rediyo BBC Hausa ɗaya daga cikin iyayen yaran ya ce ƴan bindigar sun ki su fara tattaunawa da su, inda suka ce za su tattauna ne kawai da gwamnati.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!