Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan bindiga sun kai harin ramuwar gayya a Zamfara

Published

on

Rahotonni daga jihar Zamfara na cewa, wasu ƴan bindiga sun hallaka mutane 10 a wani harin ramuwar gayya.

Kwamishinar tsaro na jihar Zamfara Abubakar Dauran shi ne tabbatar da faruwar lamarin ga Freedom Radio.

Ya ce, al’amarin ya faru ne a garin Jan Baƙo na ƙaramar hukumar Maradun, bayan da ƴan sa kai, suka hallaka wani Ɗan Fulani.

Daga nan ne, kuma suma Fulanin suka tsare wani da ya je da ji yin ice, sai Ƴan Sa kai suka shiga Jeji suka kashe Fulani uku tare da ƙona musu gidaje.

Hakan ne kuma ya sanya ƴan bindigar suka kawo harin ramuwar gayya ranar Lahadi wanda yayi sanadiyyar hallaka mutane 10.

Ku kasance da mu a Labaran An Tashi Lafiya da ƙarfe 6 na safe domin jin ƙarin bayani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!